Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi kakkausar suka kan kisan gilla da aka yi wa wata matar aure mai suna Fatima Abubakar, da ƴaƴanta shida a unguwar Chiranci da ke Jihar Kano.
Cikin wata sanarwa da fadarsa ta fitar, Shugaba Tinubu ya bayyana lamarin a matsayin mummunan rashin imani da rashin tausayi, wanda ya girgiza al’umma da ma ƙasa baki ɗaya kuma ya saɓa wa ƙa’idojin bil’adama.
Tinubu ya nuna matuƙar alhini kan wannan mummunan iftila’in, tare da miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan mamatan.
Shugaban ya kuma yaba wa rundunar ƴansandan Najeriya bisa gaggawar ɗaukar matakin da ya kai ga kama manyan waɗanda ake zargi da aikata laifin.
Ya umarci hukumomin tsaro da su tabbatar da gudanar da cikakken bincike tare da gurfanar da duk wanda aka samu da hannu a cikin kisan a gaban kotu.











