Ana ci gaba da zaman ɗar-ɗar a garuruwan Kauran Fawa da Unguwar Jika, da wasu garuruwa a ƙaramar hukumar Ɗan Ɗume a Jihar Katsina, bayan wani hari da wasu ’yan bindiga suka kai inda ake fargabar sun kashe mutum tara, tare da jikkata wasu 13.
Harin wanda aka kai cikin daren Alhamis na zuwa ne duk da sulhun da masu ruwa da tsaki a yankin suka jagoranta da ’yan bindigar, a wani yunƙuri na dawo da zaman lafiya da kare rayuka da kuma dukiyoyin al’umma.
Sai dai, hukumomin yankin sun ce sun halarci jana’izar mutum biyar, kuma suna ci gaba da ɗaukar matakai domin dawo da zaman lafiya.
Wani mazaunin ɗaya daga cikin garuruwan da abin ya shafa, wanda ya buƙaci a sakaya sunansa, ya shaida wa manema labarai cewa ƴanbindigar sun shiga garin ne a ƙafa inda suka yi ta harbi.
“Mutum tara ne suka mutu sakamakon harbin da yanbindigar suka yi, sannan 13 ne suka samu raunuka inda muka kai su asibiti domin samun kulawa. Sun ɗauki mutum aƙalla goma amma sai suka yi ta sakin mutanen sakamakon artabu. Mutum ɗaya ne ya rage a hannun su,” in ji shi.
Shugaban karamar hukumar Ɗan Dume, Bishir Hadi, ya tabbatar da afkuwar lamarin, inda ya ce tare da shi aka yi jana’izar mutanen da aka kashe.
“Mun yi sulhu kuma mun samu nasara, tsawon wata biyar ba a kawo hari ba sai yanzu. Kafin yanzu babu ranar da ba a kawo mana hari,” in ji Bishir.
Jihar Katsina da ke arewa maso yammacin Najeriya ta daɗe tana fama da hare-haren ’yan bindiga.
Duk da sulhun da gwamnatin jihar ta yi da ƴanbindigar tare da sakin wasu da aka kama, amma hukumomin na cewa matakin na daga cikin yarjejeniyoyin da wasu al’ummomin jihar suka amince da su domin samun zaman lafiya mai ɗorewa.











