Ana tsammanin haifar jarirai dubu 700 cikin shekarar 2026 a Kano – Gwamnati

Wasu alƙaluma da gwamnatin jihar Kano ta fitar ya nuna cewa jihar na tsammanin samun jarirai sabbin haihuwa aƙalla dubu 600 zuwa 700 da za a haifa cikin shekarar da muke ta 2026.

Alƙaluman wanda shugaban hukumar kula da asibitoci na jihar Dr Mansur Mudi Nagoda ya sanar na zuwa a dai dai lokacin da jihar ta Kano mafi yawan jama’a a yankin arewacin Najeriyar ke ganin ƙaruwar yawan jama’a.

Wasu bayanan baya-bayan nan sun nuna yadda yawan jama’ar jihar Kanon ya ƙaru da kashi 3.5.

A jawabinsa yayin bikin yaye ɗalibai na kwalejin kimiyya da Fasaha ta Sardauna da ke jihar, Dr Nagode ya ce duk da yawan jama’ar jihar akwai kuma tarin ƙalubalen lafiya da ya dabaibaye al’umma wanda ke nuna buƙatar jami’an lafiya don bayar da kulawa.

Dr Nagoda, ya yi gargaɗin cewa adadin jami’an lafiyar da jihar ke da su sunyi matuƙar kaɗan ga yawan al’ummarta, lura da yadda jama’ar ke ci gaba da ƙaruwa a kodayaushe.

A cewar shugaban hukumar kula da asibitocin na jihar Kano, yanzu haka jihar na fuskantar ƙarancin jami’an lafiya aƙalla dubu 4.

Dr Nagoda ya kuma roƙi makarantar horar da ɗaliban jinya da sauran ɓangarorin kiwon lafiya da su mayar da hankali wajen bayar da horo a aikace don ganin ɗaliban sun samu ƙwarewar da ta kamata wajen bayar da gudunmawa a cikin al’umma.

Akwai bayanan da ke nuna cewa jihar ta Kano na shirin ɗaukar sabbin jami’an lafiya zuwa wasu yankuna da basa samun kulawar da ta kamata ciki har da ƙananan hukumomin Doguwa da Rogo da Sumaila.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com