Home Labarai Turkiyya za ta tallafawa Nijeriya ta yaki matsalar Tsaro

Turkiyya za ta tallafawa Nijeriya ta yaki matsalar Tsaro

Shugaban ƙasar Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan ya ce ƙasarsa a shriye take ta taimakawa Najeriya wajen yaki da ta’addanci, yayin da ƙasar ke neman taimakon ƙasashen duniya don magance matsalolin tsaro da suka haɗa da ƙaruwar satar mutane a baya-bayan nan.

Erdogan ya yi wannan bayani ne a taron manema labarai tare da Shugaban Najeriya, Bola Tinubu, a birnin Ankara, inda ya ce “Turkiyya a shirye take ta raba ƙwarewar da take da ita a fannin tsaro da yaki da ta’addanci domin taimakawa Najeriya.”

Tinubu ya bayyana cewa taimakon zai haɗa da “horon soji da na tattara bayanan sirri, da kuma ayyukan yaƙi da ta’addanci”.

Shugabannin biyu sun tattauna kan bunƙasa haɗin gwiwar tattalin arziki, inda shugaba Erdogan ya ce Turkiyya za ta ƙulla kasuwancin dala biliyan 5 da Najeriya.

Bugu da ƙari, ƙasashen biyu sun sanya hannu kan wasu yarjejeniyoyi takwas a fannonin tsaro da ilimi da ci gaban al’umma da haɗin gwiwar ƙungiyoyi da sauransu.

A shekarar 2024, Najeriya ta sayi jiragen yaƙi marasa matuƙa 43 daga Turkiyya kuma ta tura sojoji 46 domin samun horo.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
COAS Ya Bukaci Bojojin Nijeriya da su Mayar da Hankali Wajen Kare Rayukan Fararen HulaTURA TA KAI BANGO: Bayan Mutuwar Bashar Sani, Dole ne Arewa Ta Fuskanci MatsalolintaDangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige Fubara
X whatsapp