Rundunar Sojin Najeriya a karkashin operation haɗin kai ta sanar da jagorantar dawowar ‘yan gudun hijirar Najeriya daga Jamhuriyar Kamaru zuwa Jihar Borno cikin tsaro.
A cewar sanarwar da ta fitar, a ranar 27 ga Janairu, 2026, sojojin tare da hadin gwiwar dakarun ƴan sa kai ta CJTF da ‘yan banga na gari sun samar da cikakken tsaro yayin da ‘yan gudun hijirar ke ƙetare iyaka daga Kirawa zuwa garin Pulka a ƙaramar hukumar Gwoza.
Wasu daga cikin wadanda suka dawo sun shafe sama da shekaru 11 a gudun hijira sakamakon rikicin ‘yan ta’adda.
Aikin dawo da ‘yan gudun hijirar ya fara ne daga Minawawu a Kamaru zuwa Moruwa kafin shiga Kirawa a Najeriya.
An gudanar da aikin bisa ƙa’idojin jin kai da tsaro, tare da hadin gwiwar Hukumar Kula da ‘Yan Gudun Hijira ta Kasa da gwamnatin jihar Borno da sauran hukumomin tsaro.
Wata babbar tawaga daga gwamnatin jihar karkashin jagorancin Wakilbe, wakilin gwamna Babagana Umara Zulum, ta halarci taron tare da wakilan UNHCR da IOM.
Kwamandan dakarun ƴan sa-kai ta CJTF, Birgediya Janar Nasiru Abdullahi ne ya tarbe su kafin a raka su zuwa cibiyar karɓar baƙi a Pulka.
A can ne aka yi musu rijista inda aka raba musu tallafi da suka hada da kuɗade da tabarma da gado daga gwamnatin Borno da kayan abinci daga gwamnatin tarayya, da kuma tallafin kudi daga UNHCR.
Rundunar Sojin ta tabbatar da cewa aikin ya gudana lafiya ba tare da wata matsala ba.











