Home Labarai Gwamnatin Kogi ta ba da umarnin rufe makarantun firamare da na sakandare...

Gwamnatin Kogi ta ba da umarnin rufe makarantun firamare da na sakandare a jihar

Gwamnatin jihar Kogi ta bayar da umarnin rufe makarantun firamare da na sakandare a faɗin jihar, wani mataki da ta ce ta ɗauka don kare lafiyar ɗalibai da kuma malamansu.

Wata sanarwa da kwamishinan yaɗa labarai na jihar Kingsley Fanwo ya fitar, ya ce an ɗauki matakin ne saboda wasu bayanan sirri na tsaro da suka samu, inda suka ga ya dace a ɗauki matakan kare makarantun.

Fanwo ya ce ba a rufe makarantun ba don tayar da hankalin ɗalibai, amma saboda kare lafiyarsu ba wai sai wani abu ya faru ba.

Ya ƙara da cewa gwamna Usman Ododo ya umarci dukkan hukumomi da abin ya shafa da su ɗauki matakai na tabbatar da cewa an koma karatu da zarar an ga babu wani haɗari.

Kwamishinan ya yaba wa jami’an tsaro kan bayar da bayanan sirri a kan lokaci, inda ya kwatanta cewa hakan zai taimaka wa tsarin tsaron jihar.

Ya tabbatar wa mazauna jihar cewa gwamnati na iyaƙar koƙarinta wajen shawo kan lamarin, inda ya ce jami’an tsaro na aiki tukuru don gano da kuma kaƙƙaɓe maɓoyar ɓata-gari a faɗin jihar.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp