Home Labarai Amurka ka iya sake kai Hari Nijeriya muddin aka ci gaba da...

Amurka ka iya sake kai Hari Nijeriya muddin aka ci gaba da kashe kiristoci- Trump

Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewa zai iya sake ƙaddamar da hare-hare a Najeriya matuƙar bai gamsu da ƙoƙarin ƙasar ba wajen daƙile hare-hare a kan kiristoci.

Trump ya bayyana haka ne a ranar Alhamis a lokaci da yake jawabi a ranar addu’a ta ƙasar Amurka karo na 74, wadda aka yi a birnin Washington.

“Duk wanda ya kai wa kiristoci hari, ya san dole Trump zai mayar da martani mai zafi. Na san maganar babu daɗi, amma ita ce magaar gaskiya,” in ji shi.

A lokacin taron addu’ar, Trump ya bayyana zuwan uwargidan Shugaban Najeriya, Remi Tinubu a addu’ar, inda ya yaba mata, sannan ya ce mata ce mai mutunci da ƙima.

Trump na bayani ne kan zargin da ake yi cewa ana yi wa kiristoci kisan kiyashi a Najeriya, lamarin da Amurka ta sa baki, har ta ƙaddamar da hare-hare a ƙasar a bara.

Sai dai Najeriya ta sha nanata cewa kashe-kashen da ake yi a ƙasar ba su da alaƙa da bambancin addini ko ƙabilanci, sannan ta ƙara da cewa tana ƙoƙarinta na magance matsalar.

Trump ya ce hare-haren da ya kai a Najeriya, ya yi ne tare da haɗin gwiwar hukumomin Najeriya, inda ya ce ya amince a kai harin ne domin fatattakar mayaƙan IS.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp