Majalisar Dattawan Najeriya ta kafa kwamtin da za su yi nazari kan gyaran dokar zaɓe inda da naɗa mambobi 12 da za su yi aiki tare da Majalisar Wakilai.
Wannan mataki ya zo ne a lokacin da majalisar ke fuskantar ƙarin matsin lamba kan amincewa da wajabcin tura sakamakon zaɓe ta na’ura kai tsaye daga rumfunan kaɗa ƙuri’a yadda mutane za su iya gani.
Shugaban Majalisar, Godswill Akpabio ya bayyana cewa an naɗa wadannan mambobi ne domin samar da kyakkyawar fahimta tsakanin majalisun biyu, da kuma tabbatar da cewa duk wani gyara da za a yi zai amfanar da dimokuradiyya a ƙasar.
Ana sa ran waɗannan mambobi za su tattauna kan dukkan abubuwan da suka janyo ce-ce-ku-ce, musamman yadda za a tabbatar da gaskiya da sahihancin sakamakon zabe.











