Home Labarai Kwankwasiyya ta yi martani kan matakin majalisar Amurka na hukunta Kwankwaso

Kwankwasiyya ta yi martani kan matakin majalisar Amurka na hukunta Kwankwaso

Ƙungiyar Kwankwasiyya a jihar Kano ta mayar da martani kan ƙudurin da wasu mambobin majalisar wakilan Amurka suka gabatar na a hukunta jagoranta Musa Kwankwaso dangane da zargin musguna wa Kiristoci a Najeriya.

A cikin wata sanarwar da ta fitar, ƙungiyar ta ce “duk da cewa tana sane da muhimmancin damuwar ƙasashen duniya kan batutuwan haƙƙin dan’adam da ‘yancin addini, amma kuma Najeriya ta kasance ƙasa mai yalwar al’adu da addinai, kuma tana fuskantar matsalolin tsaro masu sarƙaƙiya da ke shafar kowane ɓangare ba tare da bambancin addini ko ƙabila ba.”

A ranar Laraba ne wasu ‘yan majalisar wakilan Amurka suka gabatar da ƙuduri a zauren majalisar suna bukatar a sanya takunkumi kan Kwankwaso da wasu kungiyoyi da suka kira na “‘yan bindiga” wadanda suka zarga da taimakawa wajen cusguna wa mabiya addinin Kirista a kasar.

Sai dai kungiyar ta Kwankwasiyya ta bayyana Sanata Rabiu Musa Kwankwaso a matsayin ɗaya daga cikin manyan masu fafutukar tabbatar da zaman lafiya da haɗin kan kasa.

Ta ce “yana da goyon bayan al’ummomin addinai daban daban, kuma a kullum yana inganta juriya da fahimtar juna tsakanin mabambantan ɓangarori.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp