Home Labarai Gwamnatin Najeriya da gwamnonin APC sun bai wa ƴan kasuwar Singer tallafin...

Gwamnatin Najeriya da gwamnonin APC sun bai wa ƴan kasuwar Singer tallafin biliyan 8

Gwamnatin Najeriya ta bai wa ƴan kasuwar Singer tallafin kuɗi naira biliyan 5 domin rage raɗaɗin mummunar gobarar da ta ƙone kasuwar bayan wata gobara da ta tashi a cikin kasuwar.

Mataimakin shugaban ƙasar Kashim Shettima ne ya jagoranci wata tawaga zuwa jihar Kano wadda shugaban ƙasa Bola Tinubu ya aika jihar domin jajantawa waɗanda ibtila’in gobarar ya shafa.

A lokacin da yake jawabi cikin dandazon ƴan kasuwar Kashim Shettima ya jajantawa ƴan jama’a tare da sanar da tallafin da gwamnatin tarayya ta bai wa ƴan kasuwar na Naira biliyan 5.

Shettima ya ce gwamnonin jam’iyyar APC 29 sun bada tallafin naira biliyan 3 ga wadanda suka tafka wannan asara, inda ya ce za su miƙa jimillar kuɗi naira biliyan 8 ga gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf domin a hada kwamitin da za a tallafawa ƴan kasuwar.

“Bugu da ƙari, gwamnoninmu na APC guda 29 suma sun kawo tallafin biliyan 3. A taƙaice jama’a, Insha Allah za mu damƙawa gwamnan jihar Kano naira biliyan 8, zai haɗa kwamiti”

Mataimakin shugaban ƙasar Kashim Shettima ya ce Kano ita ce cibiyar Arewa don haka za su haɗa hannu domin ganin cewa sun ceto al’umma.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp