Home Labarai Sojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi...

Sojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta’addanci

Gwamnatin Najeriya ta bakin kakakin ma’aikatar tsaronta ta tabbatar da isowar sojojin Amurka aƙalla 100 cikin ƙasar ta yammacin Afrika don taimaka mata a yaƙin da ta ke da ƴan ta’addar da ke kaiwa jama’a hare-hare.

Kakakin shalkwatar tsaron Najeriyar Manjo Janar Samaila Uba ya ce tabbas sojojin Amurkan sun shiga Najeriyar amma ba za su shiga fagen daga don yin yaƙi ba, face aikin horar da dakarun Najeriyar dabarun yaƙi da ƴan ta’addan.

Isowar sojojin Amurka na zuwa bayan tun farko Donald Trump ya zargi Najeriyar da gazawa wajen baiwa Kiristoci kariya daga hare-haren da ƴanta’addan da ya kira da Musulmai ke kaiwa a sassan ƙasar.

Sai dai tuni gwamnatin Najeriya ta musanta wannan zargin bayan da ta ce ƴan ta’addan na kashe dukkanin ɓangarorin Musulmai da kuma Kiristoci kuma dakarunta na aiki tuƙuru wajen yaƙi da su musamman a yankin arewa maso yammaci da kuma arewa maso gabas.

Amurkan ta kai hare-hare cikin watan Disamba kan yankunan da ta ce a nan ne mayaƙan IS suke a yankin na arewa maso yammacin Najeriyar kuma tun daga wancan lokaci bayanai ke cewa akwai sojojin na Washington da jiragen yaƙinta da ke shawagi a sassan Najeriyar don yaƙi da matsalolin tsaron.

Cikin kwanakin baya-bayan nan anga tarin jiragen yaƙin Amurka ɗauke da ko dai sojoji ko kuma makamai na isa sassan jihohin arewacin ƙasar kamar yadda bayanan bin diddigin da kafar Reuters ke yi suka bayyana.

Tun a farkon watan nan ma’aikatar tsaron Najeriyar ta ce tana tsammanin isowar ƙarin Sojin Amurka 200 zuwa ƙasar.

Najeriya mai yawan jama’a fiye da miliyan 240 na da rinjaye mabiyan addinin Islama ne a yankin arewaci yayinda mabiya addinin Kirista ke a yankin kudanci.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp