Tallafi: Buhari ya Bada Umarnin Raba Kayan Abinci Ga ‘Yan Nijeriya

President-Muhammadu-Buhari

 

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ba da umarnin cewa a gaggauta sakin tan 40,000 na kayan Abinci daga asusun ajiyar hatsi na Gwamnatin Tarayya, domin taimakawa marasa karfi a yayin gudanar da bukukuwan Easter da sallah.

Ministan Noma da Raya Karkara Muhammed Mahmoud ne ya bayyana hakan a yayin da yake ganawa da manema labarai na Fadar Shugaban Kasa bayan wata ganawar sirri da Shugaba Muhammadu Buhari a fadar sa dake birnin tarayya Abuja a ranar Talata.

Mahmood, yace Shugaba Buhari ya bashi umarnin raba kayayyakin ga Al’ummar Nijeriya, ya kuma bayyana cewa yana fatan rabon kayan abincin zai ragewa Al’umma radadin hauhawar farashin kayan masarufi.

Ya kara da cewa, ton dubu 12 daga cikin dubu 40 da aka amince dasu za’a baiwa ma’aikatar kula da jin kai da bala’oi da ci gaban jama’a ta tarayya domin rabawa ‘yan gudun hijira a fadin kasar nan.

Economic Confidential ta rawaito ministan na cewa za’a yi amfani da tsarin da aka bi a lokacin kullen Corona (covid-19) a shekarar 2020, wajen raba ton dubu 70 na kayan abinci a wasu jihohin ciki har da birnin tarayya Abuja.

“Idan dai zaku iya tunawa, lokacin kullen corona a kasar nan shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bada umarnin fidda hatsi domin rabawa masu karamin karfi a Nijeriya.

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1190 days 11 hours 40 minutes 38 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1172 days 13 hours 22 minutes 3 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com