Tsohon Shugaban Mulkin Soji Yakubu Gowon ya kaddamar da sabbin Gidajen Radiyo da Talabishin mallakin hukumar kula da Masu Yiwa Kasa Hidima ta NYSC.
Gidan Radiyon na NYSC mai mita 88.3 fm da kuma gidan TV dake ka channel 365 akan TSTV.
Kaddamar da tashoshin da ya gudana a harabar hukumar kula da masu yiwa kasa hidima ta NYSC ya sami halartar tsohon shugaban Najeriya Janar Yakubu Gowon, Ministan Wasanni da Matasa Sunday Dare, Tsoffin Daraktocin Hukumar, masu rike da sarautun gargajiya da sauran manyan mutane a fadin Nijeriya.
Read Also:
A jawabin sa, Yakubu Gowon ya yaba da kokarin Janar Shu’aibu Ibrahim, wanda karkashin shugabancin sa ne wannan hukuma ta sami gagarumar nasarar kafa gidan Radiyo da Talabishin.
Tun bayan kafa wannan hukuma tsahon shekaru 49, ta ciga da yaye matasa masu nagarta wanda ke kai kasar ga tudun muntsira.
Da yake jawabi tun da fari Babban Daraktan Hukumar Janar Shu’aibu, ya bayyana cewa samar da kafafen yada labaran na Radiyo da talabishin na matsayin wani bangare na inganta ayyukan hidimar kasar.
Yace dukkan kafafen na NYSC Radio da NYSC TV Mambobin hukumar hidimar kasar ne za suke sarrafasu da kuma wasu cikin ma’aikatan hukumar; haka kuma masu hidimar kasa dake da Muradin samun ilimi a fannin na aikin yada labarai suma suna da dama a kafafen.
By PRNigeria Hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 18 hours 24 minutes 28 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 20 hours 5 minutes 53 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com