Kungiyar ma’aikatan jinya da Ungozoma ta kasa (NANNM), reshen birnin tarayya Abuja, ta bukaci a yi adalci bisa cin zarafin da akayi kan mambarta Abalu Marvis ta asibitin kasa dake Abuja.
Shugabar kungiyar, kwared Deborah Yusuf ce ta bayyana hakan yayin da take ganawa da manema labarai a ranar juma’a, inda tayi zargin cewa Dr. Atinko-Sunday Ikeya na asibiti ya afkawa Marvis yayin da take tsaka da lura da marasa lafiya.
Read Also:
Ta kara da cewa a ranar 13 ga watan yuni, Ikeyi yayi fatali da duk wata ka’ida ta aikin likitanci da ya kuma yi amfani da damar wajen cin zarafin ma’aikaciyar jinyar dake tsaka da aiki a matsayin abokiyar aikin sa.
Debora Yusuf tace, Jami’ar jinyar da likitan ya wulakanta, na tsaka da kula da wani mara lafiyar, likitan yace lallai sai ta bar wannan ta koma kan wanda ya uwace ta, wannan ya sanya har ta kai ga yaci zarafin ta.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 19 hours 54 minutes 41 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 21 hours 36 minutes 6 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com