A ranar Juma’a 1 ga watan Julin shekarar 2022, rahotannin suka tabbatar da cewa an wallafa Kur’anin na farko da aka fassara cikin harshen Igbo a Nijeriya.
Kur’anin da aka masa lakabi da “Nso Koran” an kaddamar da shi ne a masallacin Ansar-Ud-Deen dake birnin Abuja, inda ta cikin wata ganawa da mawallafin Littafin Muhammad Murtala Chukwuemeka ya bayyanawa sashen BBC cewa ya dauki tsawon shekaru biyar (5) kafin ya kammala fassarar daga harshen larabci zuwa harshen Igbo.
A yayin da al’umma ke tufa albarkacin bakin su kan wannan kokari na fassarar kur’anin a kafafen sadarwa na zamani, sun bayyana cewa za’a iya samun sabani kan wanda a Zahiri ke da ikon bugar kirjin cewa shi ne farkon wanda ya fassara Al’kur’ani mai girma zuwa harshen na Igbo.
Babban mai tace labarai na jaridar Daily Nigeria, Jaafar Jaafar, yace wannan yabo kai tsaye zai je ne ga farfesa Jumbo Ugoji wanda shine mutum na farko da ya fara fassara Kur’ani mai tsarki a shekarar 1984.
“‘Yar sa, Ngozi Ugoji, ta ja hankali na kan wannan batu, inda ta ce ikirarin Shiek Chukwuemeka ba daidai bane, ta kuma tura min bangwan Kur’anin da wasu shafuka” Jaafar Jaafar ya wallafa a shafin sa na Facebook.
Wannan Magana kuwa ta kara sanya al’umma da dama tofa Albarkacin bakin su.
Dake na guda cikin Aikin Jaridar PRNigeria gudanar da binciken kwakkwafi domin tabbatar da sahihancin labari, kawo yanzu dai binciken na PRNigeria ya tabbatar da cewa babu cikakken bayani akan batun cikin kafar yanar gizo.
Amma duk da haka PRNigeria da tattara wadanan siyakin bayanai
Read Also:
- An dai fassara kur’ani na farko cikin harshen Igbo a 1988 kamar yadda muka bankado a shafin Amazon da kuma, rubutaccen Kur’anin game bukatar dauka. Wanda Islam International Publications Limited suka wallafa Kuma Raqeem Press dake Islamabad da Surrey suka Buga.
- Haka kuma ko a martini da Al’umma sukayi a shafin Facebook babu wanda ya musanta cewa ba Farfesa Jumbo Ugoji ne ya fara fassara kur’anin cikin harshen Igbo ba.
- Farfesa Ugoji ya fassara cikakken Al’kur’ani mai tsarki, wanda ke kunshe ta shafuka (919), wanda kungiyar Islama ta kasa da kasa fannin Darikar Ahmadiyya ta dauki nauyi. dake an san Darikar ta Ahmadiyya da daukar nauyin fassara kur’anin cikin wasu harsuna Nijeriya musamman Yarbanci a shekarar (1957), haka kuma ta dau nauyin fassarar cikin Harsen Ibgo (1988) da harshen Hausa (1992); wadannan baya ga harsuna sama da 72 a duniya da ta dauki nauyin su.
- Kwafin Kur’anin da Farfesa Uguji ya fassara, daga harshen Turanci zuwa harshen Igbo, wanda yanzu haka na yanar gizo, yana da lamba tabbatar da ingaci ta ISBN 1 85372 047 x.
- Farfesa Jumbo Ugoji musulmi ne kuma an rawaito cewa yanzu haka yana raye.
- Kwafin fassarar ta Jumbo na cikin jerin littafai a shafin yanar gizo na Amazon, yana kuma da shafi 919 kuma an wallafa shi a shekarar 1988. (ko da yake yanzu haka ya kare akan rukunin yanar gizon).
- Lambar tabbatar da ingancin Littafi da ta ISBN da Amazon ta bawa wancen littafin da Jumbo ya fassara sun hadar da ISBN-10 1853723088 and ISBN-13 978-1853723087.
- Jaridar PRNigeria ta gano cewa Sheik Chukuemeka Malamin Majami’a ne dan Darikar “Deeper Life” kafin ya musulunta a shekarar 1989.
- Chukeuemeka ya sami nasarar musuluntar da sama da mutum 300, tun bayan da ya fara kira zuwa shiga Addini Musulun (Da’awa).
- chukuemeka ya fassarara Alku’anin mai tsarkin ne daga harshen larabci zuwa zuwa harshen Igbo.
Harshen Igbo na guda cikin harsunan Nijeriya da Al’ummar dake yankin Kudu Maso Gabashin kasar ke amfani da shi, wanda mafi yawa cikin Al’ummar yankin mabiyar Addinin kiristanci ne.
Nijeriya dai itace kasa mafi yawan Al’umma a Nahiyar Afirka, galibin Al’ummar dake zaune a Arewacin kasar musulmi ne, inda Kudancin kasar yafi yawan Kiristoci.
PRNigeria na cigaba da bincike kan wannan batu haka kuma da zarar ta sami wani cigaba a kan sa zata sanar da ku.
By PRNigeria
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 14 hours 18 minutes 26 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 15 hours 59 minutes 51 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com