Home DUNIYA Shugaban kasar Afirka ta Kudu yace sun Damuwa da yadda kasashen duniya...

Shugaban kasar Afirka ta Kudu yace sun Damuwa da yadda kasashen duniya suka kauda kansu daga fafutukar samun yancin Yammacin Sahara

Shugaban kasar Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa ya sake jaddada goyan bayan kasar sa ga Yammacin Sahara don ganin ta zama kasa mai cin gashin kan ta daga kasar Morocco.

Ramaphosa ya bayyana haka ne lokacin da ya karbi shugaban kungiyar Polisario dake fafutukar kafa kasar Yammacin Saharar, Brahim Ghali wanda ya ziyarce shi a Pretoria.

Shugaban kasar yace suna matukar damuwa da yadda kasashen duniya suka kauda kansu daga fafutukar samun yancin Yammacin Sahara wadda kasar Morocco ta yiwa kamun kazar kuku.

Ramaphosa yace su a Afirka ta Kudu sun fahimci muhimmancin wannan fafutuka ta samun yancin kan yankin, kuma suna bayyana goyan bayan su dari-bisa-dari wajen ganin an samu nasarar yancin yankin domin baiwa jama’ar yankin abinda suke bukata.

Shugaban ya danganta fafutukar ‘yancin Yammacin Sahara da na yaki da wariyar jinsin kasarsu ta Afirka ta Kudu tayi, inda ya bayyana su a matsayin halartattun yake yaken da suka zama wajibi.

Kungiyar Polisario na fafutukar samun ‘yanci kai tun daga shekarar 1976, abinda ya sa ta fada rikici da Morocco wadda ta mamaye ta tun bayan mulkin mallakar da Spain ta yiwa yankin tsakanin shekarar 1884 zuwa 1975.

Kungiyar Polisario tace akalla kasashe 80 sun amince da fafutukar su, amma kuma Morocco taki amincewa ta bata ‘yancin kai.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Mutane 200 Sun Mutu Sakomakon Girgizar ƙasar a ColombiaShahararren Mawaƙin Najeriya, Davido ya Rubuta wa Trump Wasiƙa Kan Zaɓen Jihar OsunHukumar NHRC ta Buƙaci a Kama Malamin Addinin, Sheikh JingirRundunar sojin Najeriya ta Daƙile Shirin Ƴan Bindiga a FilatoJami'an Ƴan Sanda 10 Sun Mutu Yayin Artabu da Ƴan Bindiga a Jihar KebbiAn Naɗa ɗan Najeriya Gidado Shuaib Wakilin Matasa na IPRA-UN Gabanin GWAEFCC da "Wuce Gona da Iri" da Tambayar 2027: Shin ana Rudar da Tinubu ta Hanyar Mutanen da ke Kewaye da Shi ? Daga Yushau A. ShuaibAn Samu Gawar Yara 3 da guda 1 a Sume a Gidan Mai Maganin GargajiyaMene ne Ainihin Abin da ya faru Aka Rufe Asusun Bankunan Gwamnatin Osun ?Jami'an Tsaro Sun Ceto Mutane 308 a Jihohin Arewacin Najeriya An Kama Mutane 6 da Ake Zargin da Taimaka wa Mayaƙan ISWAP a Jihar BornoZaɓen 2027: PDP ta Miƙa Sunan Jonathan ga INEC a Matsayin ɗan Takararta na Shugaban ƙasaIyanen Babban Jami'in Kula da Harkokin Kuɗaɗen ƙungiyar ISWAP Sun Miƙa Wuya ga SojojiAna Zargin Mayaƙan Boko Haram da Kashe Sojojin Nijar 14Gombe 2027: Malamai da Mambobin APC Sun yi Allah-wadai da Sukar Rarara ga Pantami
X whatsapp