Babban Sufeton Ƴan Sandan Najeriya Usman Alkali Baba ya ce bai saɓa umarnin kotu ba sakamakon ba shi da masaniya kan wani hukunci da kotun ta yanke da ya shafi mayar da wani ɗan sanda kan aikinsa.
Wannan na cikin wata sanarwa da mai magana da yawun ƴan sandan Najeriya CSP Olumuyiwa Adejobi, ya fitar inda tace babban sufeton ya ce an sallami ɗan sandan tun a 1992, shekaru kaɗan bayan shi kansa sufeton ya shiga aikin ɗan sanda.
Ya bayyana cewa hukunci na ƙarshe wanda kotu ta yanke a 2011 zamanin wani sufeto ne daban.
Read Also:
Sai dai Usman Alkali Baba ya ce ya bayar da umarni ga kwamishinan ƴan sanda wanda ke kula da ɓangaren shari’a da ya gudanar da bincike kan wannan zargin domin duba matsayar kotu da kuma ba sufeton shawarar da ta dace ta shari’a domin ɗaukar mataki.
A ɗazu ne Babbar Kotun Tarayyar Najeriya ta yanke wa Sufeton Ƴan sandan ƙasar hukuncin zaman gidan yari na wata uku.
Mai Shari’a Justice Mobolaji Olajuwon ce ta yanke hukuncin inda ta ce ya saɓa umarnin kotu kamar yadda kafar watsa labarai ta Channels a Najeriya ta ruwaito.
Tun farko dai wani ɗan sanda mai suna Patrick Okoli ne ya shigar da ƙara inda ya ce an yi masa ritaya ƙarfi da yaji a 1992 inda daga baya kotu ta bayar da umarnin a mayar da shi kan aikinsa tare da biyansa duka haƙƙoƙinsa.
PRNigeria Hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 18 hours 3 minutes 51 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 19 hours 45 minutes 16 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com