Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta sanya ranar litinin 26 da Talata 27 ga watan Disambar 2022, da litinin 2 ga Janairun 2023 a matsayin ranar Hutun bukukuwan kirsimeti da sabuwar shekara a kasar.
Ministan cikin Gida, Ogbeni Rauf Aregbesola, ne ya bayyana hakan a madadin Gwamnatin Tarayyar Nijeriya, inda ya taya daukacin mabiya Yesu Almasihu dake kasar da kasashen ketare murnan bikin kirsimeti da sabuwar shekara.
Ya bukaci kiristoci da suyi koyi da Yesu, wajen nuna kauna da Soyayya, tausayin Al’umma, zaman lafiya wannan itace hanyar nuna kauna da murnar haihuwar sa.
Ya jaddada cewa zaman lafiya da tsaro sune ginshikin inganta tattalin arzikin da cigaba, ya bukaci kiristoci da Dukkannin daukacin Al’ummar Nijeriya da suyi amfani da lokacin wajen yiwa kasar Addu’oin kawar da matsalolin rashin tsaron daya Addabi kasar.
Daga bisani ya bukaci Al’ummar kasar su mayar da hankali a fannin tsaro ta hanyar fallasa dukkan wani abu da basu yadda da shi ba
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 22 hours 33 minutes 19 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1237 days 14 minutes 44 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com