Gwamnatin Jihar Kogi dake arewa ta tsakiyar Nijeriya ta ayyana ranar Alhamis a matsayin hutu, saboda ziyarar da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari zai kai Jihar.
Gwamnatin ta ce Buhari zai kai ziyarar ce don bude wasu ayyuka da Gwamnan Jihar, Yahaya Bello ya kammala.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Kwamishinan Yada Labaran Jihar, Kingsley Fanwo, ya fitar a ranar Lahadi a Lokoja, babban birnin Jihar.
Gwamnatin jihar ta bukaci al’ummar da su yi fitar farin dango don tarbar Shugaba Buhari.
Kazalika, Gwamnatin ta bukaci kungiyoyin kwadago da masu zaman kansu da jami’an tsaro su tabbatar da zaman lafiya ya wakana a yayin ziyarar ta Buhari.
Buhari dai na ci gaba da ziyartar jihohin Najeriya don kaddamar da ayyuka.
PRNigeria Hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 18 hours 43 minutes 40 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 20 hours 25 minutes 5 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com