Biyo bayan Nazari gami da rahotannin da suka biyo bayan zaben shugaban kasa da ‘yan majalisar tarayya a Nijeriya a ranar 25 ga watan Fabreru 2023, hukumar tsaro ta Civil Defence ta tabbatar da tsarin inganta tsaro domin samun nasarar zaben gamnoni da ‘yan majalisun jihohin mai zuwa.
Wannan na kunshe ne ta cikin wata sanarwa da daraktan yada labaran rundunar Olusola Odumosu ya fitar aka kuma raba ga manema labarai a birnin tarayya Abuja.
An tsaurara matakan tsaro domin tabbatar da cewa jami’an hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC sun sami tsaro a lokacin zaben.
Read Also:
Babban kwamandan rundunar Dr. Ahmad Abubakar Audi MNI, OFR ne ya bayyana hakan yayin da yake jawabi ga masu ruwa da tsaki kan zaben gwamnonin da ‘yan majalisun jiha, inda yace sun dauk matakin ne domin magance sake samun matsaloli a inda aka samu da kuma magance faruwar hakan a zabukan dake zuwa.
Ya tabbatar da cewa tuni aka tura jami’ai dubu 102, wadanda aka horar da su yadda ya kamata akan yadda zasu tafikas da yamutsi a taron al’umma yadda ya kamata, sarrafa jama’a da dabarun gudanar da zabe domin tabbatar da tsaro.
Ya kuma tabbatar da cewa jami’an zasu cigaba da aiki da al’ummar kasar domin karbar bayanan sirri domin shawo kan matsalolin da kaje-kazo yayin gudanar da zabe da bayan zaben.
Daga bisani Audi ya bukaci ma’aikatan zabe dasu tabbatar da sunyi aiki yadda ya kamata bisa doka da oda.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 22 hours 3 minutes 13 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 23 hours 44 minutes 38 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com