Saudiyya ta bi sahun sauran ƙasashen duniya wajen kwashe ƴan ƙasarta daga Sudan a daidai lokacin da ake ci gaba da faɗa a ƙasar.
Cikin wata sanarwa da ofishin jakadancin Saudiyya a Najeriya ya fitar, ta ce ya zuwa yanzu ƙasar ta samu nasarar kwashe mutum 2, 544.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Sanarwar ta ce cikin mutanen, 119 sun ƙasance ƴan Saudiyya, yayin da 2,425 suka fito daga ƙasashe 74, inda goma daga cikin suka ƙasance ƴan Najeriya.
Ofishin jakadanci ya ce gwamnatin Saudiyya na yin duk mai yiwuwa wajen samarwa ƴan ƙasashen da aka kwashe duk abin da ya kamata, kafin mayar da su ƙasashensu na asali.
Har ila yau, ƙasar ta Saudiyya ta ce za ta yi iya kokarinta wajen ganin ta taimaka wa sauran ƙasashe kwashe mutanensu lami lafiya daga Sudan da kuma ganin an dakatar da faɗan da komawa kan tirba madaidaiciya a ƙasar.











