Gwamnatin jihar Kano tace ta shirya tsaf domin gyara yin amfani da baguzen gine-ginen da aka rushe wajen sabunta ginin ganuwar Kano, a kokarin gwamnatin na maido da wuraren tarihi a jihar .
Wannan na kunshe ta cikin wata Sanarwar da Sakataren yada labaran gwamnan jihar kano Sanusi Bature Dawakin Tofa ya aikowa PRNigeria, inda ya ce Abba Kabir Yusuf ya ce za a yi amfani da baraguzen wuraren da aka rushe wajen sake gina Badalar, kuma ana kira ga mutanen da ba su da alaka da inda aka rushe da su guji zuwa wurin domin yan sanda da jami’an hukumar Civil defense ba zasu saurarawa duk wanda aka kama ba.
Read Also:
“Mun zagaya birnin kano domin duba wuraren da aka ruguje, kuma mun yanke shawarar yin amfani da baraguzen wuraren da aka ruguje wajen gyara badalar birnin Kano domin adana tarihi, da kawata Kano da kuma mayar da wuraren wurin yawon bude idanu da dai sauransu”. Engr. Abba Kabir Yusuf yace.
“duk wanda ba ya cikin aikin rusau ya kamata ya nisanta kansa daga wurin, domin hukumomin tsaro ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen daukar matakan da suka dace kan masu kutse da kuma wadanda suke sabawa ka’ida.” A cewar Abba Gida-gida
Gwamnan ya yi kira ga al’ummar jihar da su ci gaba da bin doka da oda tare da kai rahoto ga jami’an tsaro domin ci gaban zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar Kano.
PRNigeria hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 19 hours 44 minutes 29 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 21 hours 25 minutes 54 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com