Matakin da Kungiyar ECOWAS karkashin jagorancin shugaban Najeriya Bola Ahmad Tinubu ke shirin dauka, a matsayin mafita ga kungiyar nan ta ECOWAS abun Allah Wadai ne gamu yan Najeriya.
Ina son ku sani alaqar dake tsakanin Najeriya da Nijar, alaqa ce tamkar irin wadda ke tsakanin Kano da Jigawa, duk da cewa ita Nijar bata fita daga cikin Najeriya, ko Najeriya ta fita daga cikin Nijar ba, amma zumuncin iri daya ne.
Ku sani babbar masifa ce shirin shiga yaki ko amfani da karfin soji tsakanin Najeriya da Nijar, da sunan neman a mayar da mulki hannun farar Hula.
Ya Kamata Ku tuna cewa, Najeriya da Nijar, Addininmu daya, Kabilarmu daya, akwai auratayya da alakar kasuwanci mai karfi tsakanin kasashen biyu.
A matsayina na dan jarida, tun daga ranar da na ji anata yayata batun kokarin amfani da karfin soji tsakanin Najeriya da Nijar hankalina a tashe yake har kawo yanzu.
Na kasa gane inda aka dosa, amma daga jin gargadin da Rasha ta yiwa kasashen yamma kan juyin mulkin Nijar na fahimci lamarin dai-dai gwargwado, kuma ya alamta cewa dole sai mun tashi tsaye kan wannan lamari kar a hadamu yaki tsakanin Nijar da Najeriya.
Gudunmawar da zamu Iya bayarwa a yanzu kawai shine shawara a matsayinmu na ƴan jarida daga yankin Arewa.
Da ace nasan yadda zan tunkari wannan lamari ni kadai don kawo masalaha ko tunkarar wasu manyan Arewa masu fada aji to tabbas ba zanyi wannan rubutu a wannan dandali ba. To amma Ina fatan wannan rubutu ya isa ga duk masu ruwa da tsaki na Arewa.
Ni ba masanin alakar kasa da kasa bane, amma halin yakin da aka shiga tsakanin Rasha da Ukraine shine abinda yake tsorata ni, sai kuka yakin da yanzu haka ke faruwa a Kasar Sudan.
Yadda nake ganin girman matsalar ya wuce na Iya furtata a wannan bigire.
Duk da kungiyar raya tattin arzikin kasashen Afirka ta yamma ECOWAS ta ce amfani da karfin soji shine abu na karshe da zata aiwatar, to amma ambata hakan tuni ya tunzura sojojin Nijar da suka jagoranci juyin mulki dama wasu alummar kasar.
Na lura cewar alumma da dama a Nijar sun kasa gane cewar abinda ECOWAS ta fada ba wai matsayar Najeriya ba ce kadai, a’a matsaya ce ta duk kasashen dake cikin kungiyar ECOWAS.
To amma saboda tasirin Najeriya a Afirka, tuni yan Nijar suka fara yada cewar Najeriya ce zata yaki Nijar, abinda kwata-kwata ba haka yake ba
A gefe guda amfani da karfin soji don dawo da mulkin dimukuradiyya da kasashen yamma ke kokarin tunzura ECOWAS ba abu ne da zai haifarwa da Najeriya da Arewa ɗa mai Ido ba a fahimtata.
MATAKAN DA AL’UMMAR AREWA YA KAMATA SU DAUKA
Kamar yadda masana Diflomasiyya ke yawan fada, tattaunawa da kuma bi a sannu Ita ce hanyar da akafi bukata a duk wata tinja-tinja ta kasa da kasa.
Babu Inda yaki ko nuna karfi ya taba zama masalaha face babu yadda za’a yi, don haka nake bada wadannan matakai da yakamata masu ruwa da tsaki a Arewa su dauka.
1- Yakamata mu yawaita addu’a a dukkanin wuraren Ibada na Arewa.
2- Gwamnonin Arewa masu ci da tsofaffin da sarakunan Arewa da tsofaffin shugabannin kasa da suke a raye na Arewa da kwararru a diflomasiyya na Arewa a hadu don yin taron gaggawa a samar da matsaya kan wannan lamari.
Read Also:
3- A sanya tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranci wannan zama, kasancewar yana da kyakykyawar Alaka da jamhuriya Nijar, kuma shima tsohon soja ne da ya taba mulkin soji a Najeriya kuma yayi na farar hula a tsarin dimukuradiyya, kuma makwafcin jamhuriyar Nijar ne wato dan jihar Katsina ne, kuma ana da kwarin gwiwa kan gaskiya da rikon amanar shugaba Buhari.
4- Bayan an cimma matsaya, wannan babban kwamiti na Arewa ya kira dukkan wani wakilin karamar hukuma ko Sanata dake wakiltarmu a jihohin arewa a majalisun kasa a basu sako cewar bama goyan bayan yaki, muna goyan bayan kawo karshen juyin mulkin Nijar cikin lalama da tattaunawa kuma su Isar da sakon a zauran majalisar kasa.
5 A gayyaci mamallaka kafafen yada Labarai na Arewa a fada musu matsayar Arewa kuma su yayata wannan matsaya a kafafensu na yada labarai.
6- Sarakuna su umarci Dukkanin limamai da malaman majami’a su fadakar da alumma kan Illar fadawa yaki, musamman a irin wannan lokaci da yan Najeriya ke cikin kangin talauci da matsin tattalin arziki.
7- Wannan kwamiti ya nemi dukkanin kwararrun marubuta da masu fashin baki a kafafen yada labarai na gida da ketare da shahararrun yan social media na Arewa a basu umarnin karewa da yayata matsayar da Arewa ta cimma kan batun kin amincewa a shiga yaki tsakanin Najeriya da Nijar.
8- Bayan daukar wadannan matakai tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranci tawaga zuwa ga mai girma shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu don fada masa matsayar alummar sa ta Arewa.
Kyakykyawar alakar Buhari da Tinubu zata taimaka wurin mai girma shugaba Tinubu ya saurari kukan Arewa da alummar ta.
Ina da tabbacin gogewa ta siyasa da kuma gogewa da shugaban kasa Tinubu ke da Ita zata sanya ya ji kukan alummar Arewa musamman duba da yadda ƴan Arewa suka bashi tarin kuri’u da ya zama shugaban kasar Najeriya.
9- Yan Arewa su shaidawa shugaban kasa cikakken goyan bayansu gareshi na maida mulkin farar hula a jamhuriyar Nijar, amma cikin bi a sannu da lumana da kuma tattaunawa da sojin Nijar da kauracewa duk wani yunkuri da zai haddasa yaki ko amfani da karfin soji.
10- Yan Arewa su nemi alfarmar shugaban kasa Tinubu ya amince kwamitin kin jinin yaki tsakanin Nijar da Najeriya ya tura tawaga karkashin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari zuwa Nijar don nuna musu matsayar da aka cimma a Najeriya, tare da nuna musu Najeriya bata da burin cutar da jamhuriyar Nijar.
Wadannan matakai guda 10 da na zayyana na yi sune bisa yadda nake cike da fargabar halin da Arewa zata shiga zarar mukayi sakaci aka fada yaki tsakanin Najeriya da Nijar.
Idan akabi wadannan matakai ko wasu da suka fi su dacewa na tabbatar gwamnatin tarayya zata saurari alummar Arewa kuma zata sauya ra’ayi kan batun amfani da karfin soji da kuma maida hankali kan tattaunawa ta diflomasiyya ka’in da na’in.
Ku sani Alummar Najeriya da Nijar Uwa daya ne Uba daya, kuma Hausawa na cewa zaman lafiya yafi zama dan sarki.
Ina da kwarin gwiwa kan shugaba Bola Tinubu zai saurari Alummar Arewa In aka bi wannan tsari.
Ga alummar Nijar, ku sani muna kaunarku mu yan Najeriya, domin addininmu da al’adunmu da komai namu tamkar 1 ne.
Muna da kyakykyawar alaka da ku ta sha’anin kasuwanci da zamantakewa da sauransu.
Allah ya taimaki Najeriya. Allah ya bamu lafiya da zaman lafiya a Najeriya da Nijar.
Karibullah Abdulhamid Namadobi
Kano State, Nigeria
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 19 hours 37 minutes 39 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 21 hours 19 minutes 4 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com