Babban hafsan sojin ƙasa na Najeriya, Janar Taoreed Lagbaja ya nemi afuwa daga al’ummar ƙauyen Tudun Biri da ke jihar Kaduna, kan harin jirgin maras matuƙi da ya kashe mutane a ranar Lahadi.
A wata sanarwa da rundunar sojin ƙasa ta Najeriyar ta wallafa a shafinta na sada zumunta, ta bayyana cewa babban hafsan sojin ƙasan na Najeriya ya kai ziyarar jaje a ƙauyen yau Talata inda “ya nuna nadama game da mummunan lamarin.”
Janar Lagbaja ya ce lamarin ya faru ne yayin da dakarun sama na ƙasar ke gudanar da wani sintiri ta sama, inda suka tsinkayi gungun mutane “waɗanda suka yi kuskuren fassara abubuwan da suke yi” a matsayin tamkar irin na ƴan fashi, wanda hakan ya sa aka kai musu hari.
Read Also:
Ya tabbatar da cewa za a gudanar da bincike domin “gano inda aka samu naƙasun da ya haifar da wannan mummunan abu,” inda za a yi amfani da sakamakon binciken domin daƙile faruwar irin hakan a gaba.
Al’ummar Najeriya da dama sun nuna fusata kan lamarin, wanda shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya bayar da umarnin gudanar da bincike a kai.
Tuni dai hukumar agajin gaggawa ta ƙasa ta bayyana cewa mutum 85 ne suka rasu sanadiyyar harin, yayin da wasu mutanen 60 suka samu rauni, sai dai ƙungiyoyin masu kare hakkin bil’adama na ganin cewa alƙaluman sun zarce haka.
An dai samu irin wannan kuskure a baya, inda hare-haren na sojojin Najeriya ke shafar fararen hula.
PRNigeria Hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1255 days 16 minutes 20 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1237 days 1 hour 57 minutes 45 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com