A ɗauki matakan tabbatar da amincin mata da ‘yan mata a Najeriya – UNICEF

Najeriya ta bi sahun ƙasashen duniya wajen gudanar da bikin gangamin yaƙi da zin zarafi mai nasaba da jinsi,da ƙungiyar Unicef ke jagoranta.

Gangamin na bana- mai taken ”zuba kuɗaɗe don yaƙi da cin zarafin mata da ‘yan mata” – ya jaddada ƙudurin gwamnati na magance duka nau’ikan cin zarafin mata da ƙananan yara.

Taron na bana – wanda aka kwashe kwanaki 16 ana gudanarwa ya ƙarfafa wa mutane gwiwa wajen bayyana ƙudurinsu don magance matsalar cin zarafin mata da ‘yan mata ta hanyar musayar matakan da ake ɗauka don magance matsalar a faɗin duniya.

Haka kuma gangamin ya kuma buƙaci gwamnatoci da hukumomin duniya da su bayyana irin jarin da suke zuba wa don magance matsalar cin zarafin jinsi.

Cikin wata sanarwar ta Unifef ta fitar bayan taron, ta ce nau’ikan cin zarafin jinsi da ake aikatawa a Najeriya sun haɗar da fyaɗe da cin zarafin matan aure, da aikata lalata da auren wuri da kaciyar ‘ya’ya mata da sauran abubuwa, lamarin da ke tasiri ga matan ta fuskar tunani da zamantakewa da tattalin arzikinsu.

Sanarwar ta ce gwamnatin Najeriya ƙarƙashin ma’aikatar lafiya da ma’aikatar harkokin mata, sun haɗa hannu da hukumar Unicef da sauran masu ruwa da tsaki wajen wayar da kan al’umma wajen magance matsalolin da suka jiɓanci cin zarafin mata.

Wakiliyar Unicef a Najeriya, Cristian Munduate ta ce ”a hukumarmu mun fahimci cewa magance matsalar cin zarafin mata da ‘yan mata ba abu ne da ke buƙatar gaggawa ba, babbar buƙatarmu ita ce aiki da gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki don magance matsalar tun daga tushe. A yanzu lokacin ɗaukar mataki ya yi, domin tabbatar da cewa mata da ‘yan mata sun rayu cikin aminci da karimci da girmamawa tare da ‘yanci”.

PRNigeria Hausa

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1255 days 6 hours 21 minutes 43 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1237 days 8 hours 3 minutes 8 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com