Kungiyar sanatocin Arewa ta yi Allah-wadai da kashe-kashen mutane da ake yi a jihar Filato, inda suka bukaci hukumomin da abin ya shafa su fara bincike.
Kawu ya kara da cewa, Sanatocin sun jajantawa iyalan wadanda abin ya shafa, da ‘yan uwa, da jama’a, da kuma gwamnatin jihar Filato.
Read Also:
“Abun da ya faru tabbatar abun bacin rai ne, kuma mun tsaya tsayin daka kan kudurinmu na neman adalci. A matsayinmu na yan majalisa, muna yin Allah wadai da wannan mummunan aiki, muna kuma kira ga hukumomi da su gaggauta fara gudanar da cikakken bincike.
Bayar da kayan aikin da suka dace don gudanar da bincike da nufin ganowa da kuma kamo masu laifi shi ne mafi mahimmanci. Masu laifin dole ne su fuskanci hukuncin, tare da tabbatar da adalci.
a kara da cewa Sanatocin basu ji dadin faruwar wannan lamarin ba a cikin wannan mawuyacin yanayi, hadin kan ‘yan kasa na da matukar muhimmanci, yana mai cewa “a matsayinmu na wakilan jama’a, muna kira ga gwamnatin tarayya da ta hada rahoton bincike na wannan lamari, ta kuma dauki matakin da ya dace don hana afkuwar hakan a nan gaba.
PRNigeria Hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 18 hours 37 minutes 36 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 20 hours 19 minutes 1 second
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com