Kimanin yara takwas sun mutun bayan ƙasar gini ta rufta musu a mahaƙar ƙasar ginin ta Dustin Dukku da ke unguwar Badariya a ƙaramar hukumar Birnin Kebbi a jihar Kebbi.
Shugaban ƙaramar hukumar Hon. Muhammad Dahiru Ambursa, ya tabbatar wa da sashen hausa na BBC faruwar lamarin, inda ya ce tuni aka fara shirye-shiryen yi wa yaran jana’iza.
Ya kuma ce akwai wasu ƙarin yara biyu da suka jikkata ciki har da wanda ya karye a ƙafa.
To sai dai wani mutum da abin ya faru a gaban idonsa ya shaida cewa yara tara ne suka rasu, lokacin iftila’in da ya faru da safiyar ranar Asabar
Read Also:
Shugaban karamar hukumar ya ce mafi yawa daga cikin yaran da lamarin ya rutsa da su almajirai ne waɗanda ke aikin haƙar ƙasar gini a yankin.
Honarabul Ambursa ya ce ya bayar da umarnin dakatar da haƙar ƙasar gini a wurin.
”Mun bayar da umarnin killace wurin da waya tare da saka alamar da ke nuna cewa an hana haƙar ƙasar gini a wurin, mun kuma buƙaci hakimai da sauran iyayen ƙasa da su saka a yi shela, don hana mutane haƙar ƙasar gini a wannan wuri”, in ji shi.
Masu ƙaramin ƙarfi dai kan yi amfani da ƙasa wajen yin bulon ƙasa da za su yi amfani da shi wajen yin gine-ginen musamman a garuruwa da ƙauyuka a Najeriya.
PRNigeria Hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 23 hours 21 minutes 42 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1237 days 1 hour 3 minutes 7 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com