Gwamnatin Najeriya ta sake jaddada cewar babu batun luwaɗi da maɗigo a cikin yarjejeniyar Samoa da suka sanya hannu akai a ƙarshen watan yunin da ya gabata, kamar yadda wasu ƴan ƙasar ke zargi.
Ministan watsa labaran Muhammmad Idris ya shaidawa hakan, inda yace yarjejeniyar ta kunshi ayyukan ci gaban al’umma ne, kuma an yi ta ne a tsakanin ƙasashen Afrika da na yankin Caribbean, da mutanen Pacific wato OACPS.
Haka kuma Minisitan yada labaran Muhammmad Idris ya ce akwai wata yarjenejiya mai suna OACPS da ta samu goyon bayan ƙasashen Turai da suka sa mata hannu a lokacin da ake taron majalisar ɗinkin duniya na 73.
Ya ci gaba da cewa “Akwai ƙa’idoji har 103 da aka cimma kan wannan yarjejeniya, amma babban al’amari da ya kamata a fahimta a nan shi ne, an yi waɗannan yarjejeniyar ne bisa tsarin shari’a da zai ba da damar haɗin gwiwa tsakanin OACPS da Tarayyar Turai domin cigaban al’umma, da dakile sauyin yanayi, da samar da kuɗaɗen zuba jari, ba wai yadda mutane ke ta yaɗawa ba.
Read Also:
Muhammad Idris ya ce ‘Ko kadan babu gaskiya a cikin wannan zargi, don kafin su saka hannun kan waɗannan ƙa’idoji 103 sai da aka kafa kwamiti da ya yi taza da tsifa a kansu, wanda ministan kasafin kuɗi Atiku Bagudu ne ya jagoranci kwamitin, sannan akwai ministan harkokin wajen Najeriya, da Ministan shari’a wanda kuma sai da suka tabbatar da cewar babu wata ƙa’ida daga cikin ƙa’idojin da ta ci karo da dokokin Najeriya sannan aka amice da saka hannun” in ji ministan.
Haka kuma ya ce “ya zama wajibi mu tabbatar wa da ‘yan Najeriya cewar Najeriya, da gwamnatin Bola Tinubu ba za ta saka hannu kan wata yarjejeniya ba da za ta ci karo da muradan mutanenten ƙasar nan ba ” A cewar Ministan Yaɗa Labarai Mohammed Idris.
A ranar Laraba ne wasu rahotonni suka ambato cewa gwamnatin tarayya ta saka hannu kan yarjejeniyar, wadda ta ƙunshi wasu alƙawurra tsakanin ƙasashen Tarayyar Turai, da gamayyar ƙasashen yankin Karebiya da na Pacific.
Rahotonnin sun ambato cewa baya ga ayyukan raya ƙasa da cigaban al’umma, yarjejeniyar ta kuma ƙunshi batun amincewa da gwagwarmayar neman ‘yanci da masu fafutikar luwaɗi da maɗigo ke yi a ƙasashen.
A shekarar 2014 Najeriya ta amince da dokar haramta alaƙar aure tsakanin jinsi ɗaya, abin da ke nufin luwaɗi da maɗigo haramtattu ne a ƙasar.
PRNigeria Hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 15 hours 8 minutes 35 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 16 hours 50 minutes 0 second
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com