Gwamnatin Najeriya ta gargaɗi jihohin ƙasar 18 kan barazanar ɓarkewar cutar Kwalara saboda barazanar fuskantar ambaliya, sakamakon ci gaba da ruwan sama da ake yi a jihohin.
Ministan ruwa da tsaftar muhalli na ƙasar, Joseph Terlumum ne ya bayyana damuwar a lokacin da yake jawabi ga taron manema labarai ranar Alhamis a Abuja.
Ya ce kawo yanzu mutum 63 ne suka mutu sakamakon bullar cutar, yayin da aka samu mutum 1,102 da ake zargi sun kamu da cutar.
Mamakon ruwan sama da ake samu a baya-bayan nan a wasu jihohin ƙasar na ƙara fargaba a zukatan jama’a kan ƙara bazuwar cutar, lamarin da ya sa ministan ya yi kira ga jihohin da su ƙara ƙaimi wajen tsaftace magudanar ruwa, don kauce wa ambaliya.
“Muna kira ga jihohi da ƙananan hukumomi su ƙara ƙaimi wajen tsaftace muhalli domin kauce wa ambaliya da sauran bala’o’in da ke tattare da ambaliya, kamar cutar kwalara”.
Jihohin da ministan ya ce suna fuskantar barazanar ambaliyar sun haɗa da; Akwa Ibom da Anambra da Adamawa da Benue da Bayelsa da Cross River da Delta da Edo da Jigawa da Kogi da Kebbi da Kaduna da Niger da Nasarawa da Ondo da Ogun da Rivers da Taraba da luma birnin tarayya Abuja.
PRNigeria Hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 15 hours 55 minutes 12 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 17 hours 36 minutes 37 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com