Gwamnatin Tarayya ta ayyana raba shinkafa tirela 20 ga jihohi 36 da Babban Birnin Tarayya Abuja, domin rabawa ga mabukata.
Za a raba kayan abincin ne a faɗin kasar a masatyin wani matsaki na kawar da matsalar yunwa da ke addabar kasar.
Ministan Yada Labarai da Wayar da Kan Jama’a, Mohammed Idris ne ya bayyana hakan ga manema labaran fadar Shugaban Kasa a ranar Litinin, jim kadan bayan fitowa daga taron Majalisar Zartawa wanda Shugaban Kasar, Bola Tinubu ya jagoranta.
Read Also:
Ministan ya ce majalisar ta fahimci yadda matsalar karancin abincin ke addabar ’yan kasar, don hakan ta amince da raba shinkafa tirela 20 ga kowacce jiha da Abuja ga mabukata.
Al’ummar Nijeriya dai na fama da matsalar tsadar abinci, abin da suka alakanta da cire tallafin man fetur da gwamnatin Tinubu ta yi.
Matakin dai ya haifar da tashin farashin kayan masarufi da kayan amfanin yau da kullum a kasar da ke da arzikin man fetur da ma’adinan a karkashin kasa.
PRNigeria Hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 11 hours 14 minutes 30 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 12 hours 55 minutes 55 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com