Kungiyar ƙwadago ta NLC ta sanar da amincewarta da naira 70,000 a matsayin mafi karacin albashi ga ma’aikatan ƙasar Nijeriya.
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ne ya amince da sabon albashin a ganawarsa da wakilan ƙungiyoyin ƴan ƙwadago na ƙasar a ranar Alhamis.
Wannan na zuwa ne bayan kwashe tsawon lokaci ana taƙaddama tsakanin ƴan ƙwadago da gwamnatin Najeriya game da sabon albashin mafi ƙanƙanta ga ma’aikata.
Shugaban NLC Joe Ajaero ya ce sun amince ne da tayin N70,000 saboda akwai abubuwan da ke ƙunshe da ya kira na ƙarfafa gwiwa.
Ƙungiya ta ce abin da ya ƙara ƙarfafa mata guiwa na amincewa da tayin shi ne alƙawalin da shugaban ƙasar ya ɗauka na sake duba albashin duk bayan shekara uku maimakon shekara biyar, kamar yadda mataimakin shugaban Kabiru Adamu Minjibir ya shaida wa manema labarai a fadar shugaban ƙasa.
“Sannan gwamnati za ta bayar da manyan bas bas masu ɗaukar mutum 100 wanda zai rage wa ma’aikata wahalar tafiye-tafiye,” in ji shi.
Tun janye tallafin mai da gwamnatin Bola Tinubu ta yi, ta shiga takun-saka da ƙungiyoyin ƙwadago, inda suka nemi ƙarin albashi da ya zarta kashi 300 cikin 100 sakamakon tsadar rayuwa da janye tallafin ya jefa ƴan Najeriya.
PRNigeria Hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 11 hours 41 minutes 53 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 13 hours 23 minutes 18 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com