Rundunar ‘yan sandan birnin tarayya Abuja ta bukaci matasan birni dasu karacewa shiga zanga-zanga da wasu ke shirin shiryawa a birni.
Kwamishinan ‘yan sandan babban birnin, Benneth Igweh, ne ya bukaci hakan, inda yace su kauracewa shiga zanga-zangar da ake shirin gudanarwa a farkon watan Agusta kan matsalar tsadar rayuwa da ta addabi Yan Nigeria.
Read Also:
Igwe ya bayyana haka ne Lokacin da ya ke ganawa da manema labaru a Birnin Abuja yayin da aka gurfanar da wadansu da ake zargi da aikata laifuka daban daban a yankin.
Kwamishinan ya ce ya na tsoron Kar masu aikata laifuka su yi amfani da damar zanga-zangar don kawo barazana ga tsaro da kuma lalata duniyar alumma.
Ya ci gaba da cewa jami’an tsaro na birnin tarayya na aiki ba dare ba rana don tabbatar da tsaro a yankin, in da ya ce suna bin batagari har wasu jihohi makota musamman wadanda ke zamantowa barazanane ga yankin.
PRNigeria hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 15 hours 47 minutes 3 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 17 hours 28 minutes 28 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com