Amurka da Birtaniya da Canada sun buƙaci al’ummarsu da ke zaune a Najeriya su zama masu taka-tsan-tsan inda suka yi gargaɗin yiwuwar samun tashin hankali a zanga-zangar gama-garin da ake shirin yi.
Gargaɗin ya so ne daidai lokacin da al’ummar ƙasar ke shirya zanga-zanga don nuna tura ta kai bango ga matsalolin yunwa da kuma matsin rayuwa da aka tsara somawa ranar 1 ga watan Agusta.
A wasu shawarwari da ƙasashen suka bai wa al’ummarsu da ke zaune a Najeriya, sun buƙace su da su guji wuraren da za a iya samun arangama tsakanin jami’an tsaro da masu zanga-zangar.
A na shi shawarar, ofishin jakadancin Amurka da ke Abuja ya buƙaci Amurkawa da su nesanta kansu daga gangamin inda suka shawarce su da su kaucewa shiga dandazon jama’a su kuma ƙauracewa zanga-zanga sannan su kuma riƙa sauraron labarai.
Haka zalika, ofishin jakadancin Birtaniya a Najeriyar ya yi gargaɗi cewa za a yi ganin zanga-zangar tsakanin yau 29 ga watan Yuli zuwa 10 ga watan Agusta a manyan birane kamar Abuja da Legas.
Ofishin ya buƙaci al’ummar Birtaniyar su yi kaffa-kaffa sannan su guji wuraren taron jama’a inda suka yi misali da yadda zanga-zangar da aka yi a baya ta rikiɗe zuwa tashin hankali.
Ita ma gwamnatin Canada ta shawarci al’ummarta da su bi umarnin hukumomi su kuma ci gaba da bibiyar kakafen yaɗa labarai domin sanin abin da ke wakana.
Wannan dai na nuna yadda ake nuna fargaba kan al’amura a Najeriya game da zanga-zangar da ake shirin yi da kuma tasirinta kan tsaron Najeriya.
PRNigeria Hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 11 hours 39 minutes 50 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 13 hours 21 minutes 15 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com