Gwamnatin Najeriya ta ce ta tsaurara matakan bincike a dukkan hanyoyin shigarta domin daƙile yiwuwar shiga da cutar ƙyandar biri cikin ƙasar.
Wannan na zuwa ne bayan hukumar hana yaɗuwar cutuka ta Afirka, da ma Majalisar Dinkin Duniya sun ƙaddamar da dokar ta ɓaci a kan yaƙi da cutar ta ƙyandar biri da ake kira da Mpox.
Da yake sanar da matakan da hukumomi a Najeriyar ke ɗauka domin kare jama’a daga wannan cuta, ministan lafiya Farfesa Muhammad Pate, ya ce za a tsaurara bincike a kan masu shiga Najeriya daga kowanne ɓangare, domin tabbatar da ganin wani daga waje bai shigar da ƙwayar cutar cikin ƙasar ba.
Sanarwar da Ministan ya fitar ta ce cibiyar daƙile yaɗuwar cutuka ta ƙasar ta sanar da gwamnati da cewa an samu mutum 39 da suka kamu da cutar ƙyandar biri a Najeriya.
Ministan ya ce daga alƙalumman da hukumomi suka tattara daga farkon wannan shekarar, an samu masu cutar ne a jihohi 33 da birnin tarayya Abuja, kuma kawo yanzu babu wanda ya mutu sanadiyyar cutar.
Saboda haka ne ministan ya ce gwamnati ta yi saurin samar da tsarin yin gwaji ga duk wanda zai shiga Najeriya, domin gano cutar tun kafin a shigar masu da annoba.
Itama hukumar hana yaduwar cutuka ta Najeriyar ta jaddada wannan matakin da gwamnatin tarayyar ta sanar, kuma shugaban ta Dr Jide Idris, ya yi bayanin cewa sun ƙara matakan yin gwaji a filayen jiragen saman ƙasa da ƙasa guda 5 da ake da su a ƙasar, da tashoshin ruwa 10 da kuma iyakokin kan ƙasa guda 51, duk dai a ƙoƙarin hana shiga da cutar.
Hukumomi a Najeriyar dai sun kuma sanar da tsaurara matakan tantance masu ɗauke da cutar a jihohin Lagos da Enugu da Rivers da Cross Rver da Akwa Ibom da kuma Adamawa.
Sauran jihohin sun haɗa da Taraba da Kano da kuma birnin tarayya Abuja.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 22 hours 24 minutes 33 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1237 days 5 minutes 58 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com