Hukumar kare haƙƙin mai saye ta ƙasa (FCCPC) ta bai wa ‘yan kasuwa a faɗin Najeriya wa’adin wata guda don saukar da farashin kayayyaki da kuma daina tsawwala wa masu saye.
Sanarwar ta fito ne daga bakin sabon mataimakin shugaban hukumar, Mista Tunji Bello, a yayin wani taron kwana ɗaya da masu ruwa da tsaki suka gudanar kan tsawwala farashin kayyayaki a Abuja.
Bello ya jaddada cewa hukumar ta ɗauki matakin ne da nufin magance yawaitar tsadar kayayyaki da ke addabar masu saye a faɗin ƙasar.
Ya yi nuni da cewa, yayin da hukumar ta fahimci ƙalubalen da ‘yan kasuwa ke fuskanta, akwai damuwa kan yadda ƴan kasuwar suka ƙara farashin kayayyaki da gangan da kuma ƙoƙarin haɗa kai tsakaninsu domin cin gajiyar masu saye.
“Akwai gungun ‘yan kasuwa da ke haɗa baki da kai wajen tsawwala wa masu saye” in ji Bello, inda ya buƙaci ƴan kasuwar su yi aiki da kishin ƙasa da adalci.
Hukumar ta FCCPC ta yi amfani da sashe na 155 na dokokin kasuwanci don jaddada muhimmancin matsayar ta a kan farashin riba.
A ƙarƙashin wannan sashe, mutane ko ƙungiyoyin kamfanoni da aka samu da laifin ƙara farashin kayayyaki da gangan za su fuskanci hukunci mai tsanani, gami da tara da kuma ɗauri
Bello ya yi gargadin cewa Hukumar ta shirya tsaf domin ɗaukar tsauraran matakan tsaro a kan wadanda suka keta dokar da zarar wa’adin ya ƙare.
Bello ya bukaci masu ruwa da tsaki da ƴan kasuwa da su ba su haɗin kai, tare da karfafa musu gwiwa kan su rage farashin kayayyakinsu a cikin wata guda.
Hukumar ta FCCPC ta bayyana ƙarara cewa za ta sa ido sosai kan yadda ake bin doka da oda na kasuwanci tare da fara aiwatar da dokar a kan waɗanda ke ci gaba da tsawwala wa masu saye.
Hukumar ta mayar da hankali ne wajen tabbatar da cewa farashin ya yi daidai da kuma yadda kasuwar ke tafiya yadda ya kamata domin kare muradun masu saye da Najeriya gaba ɗaya.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 18 hours 23 minutes 51 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 20 hours 5 minutes 16 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com