Hukumar bayar da agajin gaggawa ta Najeriya (NEMA) ta ce ambaliyar ruwa ta yi sanadiyar mutuwar aƙalla mutum 195 a jihohi 15 na ƙasar a shekarar 2024.
Hukumar ta kuma ce ambaliyar ta raba ƙarin wasu fiye da mutum 208,000 da muhallansu a cikin jihohi 28.
A cikin rahoton da ta fitar kan ƙididdigar ɓarnar da ambaliya ta yi a Najeriya a cikin 2024, NEMA ta ce fiye da kadada 107,000 da gidaje 80,000 ne ambaliyar ta lalata a bana.
Babbar daraktar hukumar NEMA, Hajiya Zubaida Umar, ta shaida wa manema labarai cewa: ‘‘Hasashen yanayi da muka samu daga cibiyar aikin gaggawa da muka kafa a cikin watan Yuli, ya nuna cewa ƙananan hukumomi 140 wannan ambaliya ta shafa, a cikin jihohi 28’’
‘‘Sannan mutum 548,494 ne ambaliyar ta shafa, kuma a cikinsu aƙalla mutum 2,000 ne suka ji rauni sakamakon ambaliyar’’
Hajiya Zubaida Umar ta ƙara da cewa jihohin da ambaliyar ta fi shafa sun haɗa da Bauchi da Zamfara da Sokoto da kuma Jigawa.
‘‘Jihar Bauchi ce ta ɗaya, amma a Jigawa aka fi samun asarar rayuka, amma a Bauchi da Zamfara ne aka fi tafka asarar da ta shafi sauran abubuwa’’
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1255 days 1 hour 5 minutes 36 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1237 days 2 hours 47 minutes 1 second
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com