Shugaba Bola Tinubu ya taya zaɓaɓɓen gwamnan jihar Edo, Monday Okpebholo murnar lashe zaɓe.
Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta INEC ce ta sanar da Okpebholo matsayin wanda ya lashe zaɓen da aka gudanar ranar Asabar 21 ga watan Satumba, inda ya doke sauran ƴan takara.
Wata sanarwa da mai bai wa shugaban shawara kan harkar yaɗa labarai Bayo Onanuga ya fitar a shafinsa na X, Tinubu ya yaba wa jagorancin jam’iyyar APC na ƙasa da kuma gwamnonin jam’iyyar bisa jajircewarsu wajen ganin an samu nasara.
Ya buƙaci sabon gwamnan jihar ta Edo da ya ɗauki nasarar a matsayin hakki da aka ɗora masa wajen kai jihar gaba.
“Nasarar ta nuna irin goyon baya da mutane ke yi wa jam’iyyar mu ta APC, ƙoƙari da take yi da kuma tsare-tsare da take ɓullo da su wajen inganta rayuwar ƴan Najeriya,” in ji Tinubu.
Ya ce Okpebholo ya nuna dattako wajen gayyato ƴan adawa domin a yi tafiya tare da kuma haɗa kan al’ummar jihar don samun ci gaba.
Shugaban Najeriyar ya kuma yaba yadda aka gudanar da zaɓen cikin kwanciyar hankali da lumana.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 12 hours 31 minutes 4 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 14 hours 12 minutes 29 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com