Kungiyar ci gaban al’umma ta Yiaga Africa ta caccaki sakamakon zaɓen gwamnan jihar Edo da aka gudanar a ranar Asabar, tana mai cewa zaɓen ya gaza cika ƙa’idar gaskiya da amana.
Cikin wata sanarwa da ta fitar a yau Litinin, wadda Shugabar tawagar lura da zaɓen Edo na 2024, Dr. Aisha Abdullahi da Daraktan gudanarwarta, Samson Itodo suka sanya wa hannu, sun bayyana cewa zaɓen jihar Edo na 2024 ya gaza cika ƙa’idar gaskiya saboda rashin bayyana gaskiya kan tsarin tattara sakamakon zaɓen.
Ƙungiyar ta ce yayin da aka bi ƙa’idoji a wajen tantance masu zaɓe, yin zaɓe, ƙirga ƙuri’u, da rubuta sakamako a rumfunan zaɓe, an yi maguɗi a wajen tattara sakamakon zaɓe sakamakon haɗin kai tsakanin wasu jami’an zaɓe na INEC da wasu mutane.
Wannan maguɗi, in ji su, ya lalata amincin zaɓen gaba ɗaya.
Kungiyar ta yi wannan hukunci ne bayan amfani da dabarar Process and Results Verification for Transparency, PRVT, wajen duba zaɓen gwamnan jihar Edo.
Haka kuma, sun ce sun tura masu sa ido mutum 300 da wasu masu sintiri 25 waɗanda suka zagaye rumfunan zaɓe a dukkan kananan hukumomi 18 na jihar.
Read Also:
Hukumar zaɓe ta INEC ta bayyana ɗan takarar jam’iyyar APC, Monday Okpebholo, a matsayin wanda ya lashe zaɓen bayan ya doke manyan abokan hamayyarsa Asue Ighodalo na PDP da Olumide Akpata na LP.
INEC ta bayyana cewa, ɗan takarar APC ya samu ƙuri’u 291,667, yayin da Ighodalo ya samu ƙuri’u 247,274.
Akpata na LP kuwa ya zo na uku da ƙuri’u 22,763.
Kungiyar Yiaga Africa ta ce ta samu rahotannin maguɗi da tashin hankali a yayin tattara sakamako a kananan hukumomin Ikpoba/Okha, Etsako West, Egor da Oredo.
Sun ce wannan maguɗi ya haɗa da tsoratar da jami’an zaɓe na INEC, masu sa ido, da kuma wakilan jam’iyyu.
Ƙungiyar ta kuma bayyana cewa rahotanninta sun nuna ɓarnar sakamakon da aka yi a wasu rumfunan zaɓe.
Rahoton ya ce akwai bambance-bambance tsakanin sakamakon da aka bayyana da kuma adadin ƙuri’un da aka tattara a rumfunan zaɓe.
Ƙungiyar ta ƙara da cewa wannan maguɗi ya jawo dole a ƙi amincewa da sakamakon ƙarshe na zaɓen.
Duk da haka, Yiaga Africa ta yarda da sakamakon ƙididdigar INEC kan yawan fitowar masu zaɓe da ƙuri’un da aka ƙi karɓa.
Kungiyar ta ce sakamakon INEC ya yi daidai da hasashenta na fitowar masu zaɓe tsakanin kashi 20.9 zuwa 24.1, inda hukumar ta bayyana cewa fitowar masu zaɓe ya kasance kashi 22.4.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 22 hours 11 minutes 36 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 23 hours 53 minutes 1 second
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com