Babbar kotun tarayya a Najeriya da ke zamanta a Abuja, ta haramtawa Hukumar Kula da Lafiyar Ababen Hawa ta VIO, ta daina kamawa da kwacewa ko kuma cin tarar masu ababen hawa.
Haka kotun ta umarci jami’an hukumar na VIO su daina tsaida masu ababen hawa akan hanyoyin ƙasar.
Read Also:
Mai shari’a Evelyn Maha ce dai ta yanke wannan hukuncin, bayan da Abubakar Marshal, mai rajin kare hakkin bil’adama ya shigar da ƙara kan lamarin.
A hukuncin nata ta ce, kotun ta gamsu da hujjojin mai ƙara na cewa babu wata doka da ta baiwa waɗanda ake ƙara hurumin tsaidawa da kamawa da kwacewa ko kuma cin tarar masu ababen hawa a kan hanya.
Mai shari’a Maha ta kuma bada umarnin dakatar da waɗanda ake ƙara, daga tauye haƙƙin ƴan Najeriya na yin zirga-zirga yadda suke suke so ba tare da sahalewar doka ba.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 14 hours 59 minutes 46 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 16 hours 41 minutes 11 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com