Ɗan takarar shugaban ƙasa a karkashin jam’iyyar Labour a zaɓen 2023, Peter Obi ya kwatanta sake ƙara kuɗin fetur a matsayin “abin takaici”, inda ya buƙaci gwamnatin tarayya da ta janye ƙarin kuɗin fetur da ta yi.
A wani sako da ya wallafa a shafinsa na X, Obi ya ɗora alhakin halin matsin rayuwa da ƴan Najeriya ke ciki kan gwamnatin tarayya.
Ya ce gwamnati mai ci na kawo tsare-tsare marasa kyau waɗanda ba su dace ba, inda ya ce ƙara kuɗin fetur da kamfanin mai na NNPCL ya yi ba daidai bane.
Martanin Obi na zuwa ne a daidai lokacin da NPPCL ya sanar da sake ƙara kudin mai.
“Ƙarin kuɗin fetur abin Alla-wadai ne ganin cewa ƴan Najeriya na cikin matsin rayuwa wanda gwamnati mai ci ta janyo. Bai dace a ƙara kuɗin mai ba tare da wani bayani ba,” in ji Obi.
Ya ce lamarin abin takaici ne matuka, ganin yadda hakan zai shafi ƴan ƙasar da kuma tattalin arzikinta.
“Ba haka ya kamata a lura da tattalin arziki ba, ba kuma haka ya dace a mulki ƙasa ba. Babu abin da wannan ƙarin zai janyo illa wahala ga ƴan Najeiya,” in ji Peter Obi.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 18 hours 28 minutes 30 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 20 hours 9 minutes 55 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com