Gwamnatin Najeriya ta yi hasashen kwashe kwana biyar ana mamakon ruwa, wanda zai iya jawo ambaliya a jihohi 22 na babban birnin tarayyar ƙasar, inda ta yi gargaɗi ga garuruwan da suke bakin tekunan Donga da Binue da Ogun su tashi daga yankunan.
Jaridar Punch ce ta ruwaito hakan a ranar Litinin daga ma’aikatar muhalli.
Rohoton na kwamitin bayar da gargaɗi na ma’aikatar ya ƙara da cewa za a iya fuskantar ambaliyar ne a ranar 14 da 18 na watan Oktoba.
Jihohin da yankunan da za su iya fuskantar ambaliyar sun haɗa da jihar Osun (Ede, Ile-Ife, Ilesa, Osogbo); jihar Delta (Escravos); jihar Kuros Riba (Ikom); jihar Anambra (Onitsha); jihar Taraba (Donga, Ibi, Wukari, Bandawa, Beli, Bolleri, Dampar, Duchi, Garkowa, Gassol, Gungun Bodel, Kambari, Kwata Kanawa, Lau, Mayo Ranewo, Mutum Biyu, Ngaruwa, Serti, Yorro); jihar Nasarawa (Rukubi); jihar Kebbi (Argungu, Birnin-Kebbi, Gwandu, Kalgo, Ribah, Sakaba, Yelwa); jihar Gombe (Bajoga); jihar Katsina (Bakori, Funtua); jihar Borno (Biu, Briyel); jihar Kaduna (Birnin-Gwari, Buruku, Kaduna, Jaji); jihar Niger (Bida, Kontagora, Lapai, Lavun, Magama, Mashegu, Mokwa, New Bussa, Rijau, Sarkin Pawa, Suleja, Wushishi).
Sauran su ne jihar Yobe (Dapchi); Adamawa (Demsa, Farkumo, Ganye, Gbajili, Jimeta, Mayo-Belwa, Mubi, Natubi, Numan, Song, Shelleng, Wuro Bokki); Kogi (Ibaji, Omala); Kwara (Jebba, Kosubosu); Bauchi (Kari, Tafawa Balewa, Kirfi); Plateau (Shendam); babban birnin tarayya Abuja (Kubwa, Gwagwalada, Bwari); Kano (Sumaila); Oyo (Kishi); Sokoto (Silame); da Zamfara (Majara).
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 15 hours 6 minutes 23 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 16 hours 47 minutes 48 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com