Wasu da ake zargin ƴan bimdiga sun kashe mutum biyar a wani sabon hari da suka kai karamar hukumar Bokkos na jihar Filato.
Shugaban ƙungiyar ci gaban al’ummar Bokkos, Farmasum Fuddang shi ya tabbaatr da faruwar hakan a jiya Talata.
Ya shaida wa gidan talabijin na Channels cewa irin harin ya janyo mutuwar mutane biyar bayan kwantan-ɓauna da ƴan bindigar suka yi musu.
“Harin ya yi sanadiyyar rayukan matasa huɗu waɗanda suka fito domin tsare gidajensu. Bayan nan maharan sun kuma kashe wani tsoho bayan yin dirar miƙiya zuwa cikin gidansa,” in ji Fuddang.
Harin dai na zuwa ne ƙasa da mako ɗaya da kai wasu hare-hare, inda aka kashe wasu mutane goma a karamar hukumar ta hanyar yi musu kisan gilla.
Al’ummar yankin sun yaba wa jami’an tsaro bisa ƙoƙarinsu na fatattakar ƴan bindigar, inda suka yi kira na a ƙara kaimi tare da haɗin gwiwa wajen daƙile irin waɗannan hare-hare a yankin.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 12 hours 15 minutes 29 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 13 hours 56 minutes 54 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com