Majalisar wakilai ta ja hankalin shugaban Najeriya Bola Tinubu kan yiyuwar karya tanadin dokar kashe kuɗin ƙasa idan har ya yi jinkirin gabatar da kasafin kuɗn 2025 ga majalisa.
Wannan na zuwa ne yayin da ya rage watanni biyu wa’adin kasafin 2024 ya ƙare.
Ɗan majalisar da ya gabatar da ƙudirin, Clement Jimbo, ya ja hankali cewa ya kamata a ce kawo yanzu an gabatar da kasafin kuɗin 2025 kasancewar watanni biyu kacal suka rage kafin wa’adin kasafin kuɗin bana ya ƙare.
Majalisar wakilan ta bayyana damuwa a kan ƙurewar lokacin da ya kamata a samu domin nazari kan kasafin na baɗi kafin amincewa da shi a majalisar dokokin tarayya.
Majalisar ta yi nuni da cewa doka ta buƙaci a gabatar wa majalisa ƙiyasin kasafin kuɗi aƙalla watanni huɗu kafin shiga sabuwar shekara domin samun damar tantancewa shi da kuma amincewa.
A yanzu dai majalisar ta miƙa wannan batu ga kwamitinta a kan tsare-tsaren ƙasa.
A ranar biyu ga watan Oktoba shugaba Tinubu ya bar Najeriya zuwa Birtaniya domin yin hutun makonni biyu.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 15 hours 51 minutes 47 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 17 hours 33 minutes 12 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com