Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya sake jaddada kudirin gwamnatinsa na inganta jin daɗin ma’aikatan gwamnati yayin da ya karɓi rahoton da aka jima ana jira daga kwamitin mafi karancin albashi na jihar.
Bayanin hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar aka raba manema labarai a jihar Kano a ranar Talata.
Read Also:
Kwamitin, ƙarƙashin jagorancin Usman Bala, mai baiwa Gwamna shawara kan al’amuran jiha, an ɗora masa nauyin duba da kuma bada shawarar inganta tsarin albashi mafi ƙankanta na jihar.
Yayin miƙa rahoton, Gwamna Yusuf ya nuna gamsuwarsa sosai da aikin kwamitin, inda ya yaba musu bisa cikakken bincike da tuntuɓar da suka gudanar.
Ya jaddada cewa shawarwarin kwamitin za su taimaka wa gwamnati wajen aiwatar da manufofi da suka dace da tsarin tattalin arzikin jihar kuma masu ɗorewa.
“Mun zaɓi wannan kwamiti ne saboda muna da imani da ƙarfin basirarsu wajen ba da shawarwari masu fa’ida da sabbin dabaru don ci gaba,” inji gwamnan.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 12 hours 44 minutes 27 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 14 hours 25 minutes 52 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com