Home Labarai Rushe shugabancin KANSIEC ya haifar da cece-kuce a jihar Kano

Rushe shugabancin KANSIEC ya haifar da cece-kuce a jihar Kano

Majalisar jihar Kano
Majalisar jihar Kano

Majalisar dokokin jihar Kano ta tabbatar da cewa za a gudanar da zaben kananan hukumomi kamar yadda aka tsara a ranar Asabar 26 ga watan Oktoba, 2024, duk da hukuncin da babbar kotun tarayya ta yanke na hana hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Kano KANSIEC gudanar da zaben.

Wannan matsaya ta biyo bayan hukuncin da mai shari’a Simon Amobeda na babbar kotun tarayya da ke Kano ya yanke a ranar Talata,

Kotu tace wadanda aka bawa mukamin shugabannin hukumar basu cancanta saboda sun kasance magoya bayan jamiyyar NNPP mai mulkin Kano, dan haka kotun tace wadannan mutane basu da damar gudanar da zaben Ƙananan.
Sai dai gwamnatin jihar Kano ta bayyana kudirinta na ci gaba da gudanar da zaben, ko da kuwa hukumomin tsaro irin na ‘yan sanda ba sa iya ba da kariya.

Shugaban masu rinjaye na majalisar, Lawan Hussaini Dala, ya soki hukuncin kotun, yana mai cewa ya sabawa umarnin da mai shari’a Nura Ma’aji ya bayar a baya, wanda ya haramtawa jam’iyyun siyasa 19 ciki har da jam’iyyar All Progressives Congress (APC) kalubalantar zabe.

“Hukuncin da kotun tarayya ta yanke na tsige shugaban KANSIEC ya ci karo da hukuncin da Mai shari’a Ma’aji ya yanke na hana jam’iyyun siyasa kutsawa cikin harkokin zabe,” in ji Dala.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
HOTO: NSCDC ta Tsare Jami'ai 24 Kan Mutuwar Masu Hakar Ma'adinai a TsareShirin Tallafin Mai: Atiku ya yi Watsi da Gaskiyar Magana – APCGwamnatin Tarayya ta Inganta Samar da Abinci ta Hanyar Shirin AgriShield na ONSA Daga Chido OnumahAtiku ya yi Tambaya Kan Rashin Zuwa UNGA a Karo na Uku da Tinubu ya yi, ya Nemi Karin BayaniFalconets ta Fice Daga Gasar Cin Kofin Duniya ta Mata Ƴan Kasa da Shekaru 20 Bayan Colombia ta Sha Kashi a Wasan KarsheMatawalle Ya Nemi Tallafin Czech Don Samar da Alburusan DICON da Canja FasahaRundunar Sojojin Najeriya Ta Tallafa wa Iyalan Sojojin Gambia da Suka MutuFilato: Sojoji Sun Kama Masu Garkuwa 11, Sun Kwato MakamaiOPHK ta yi Bayani Kan Rahoton Amnesty na 2016 Dangane da Mutuwar da Ake Zargi a Barkin Giwa2027: Sama da Mambobin Jam'iyyar NDC 6,000 Sun Sauya Sheka Zuwa PDP a EnuguKwankwaso ya Nuna Aniyar Yin Sulhu da Gwamna YusufYadda Hon. Hudu Kanje Ya Sake Fasalin Jagorancin Cigaban Kasa Daga Mika'il Ja'afarƳan Sanda Sun Kama Mutane 300 a Farmakin Wuraren da Ake Aikata Laifuka a FCT Sun Kwace Wukake, Bindigar Wasa, da WiwiZakari Mohammed: Dole Kwara ta Cika Kwarewarta – Dan Takarar ADC ya Nemi Muhawara a BayyaneWSCIJ ta Yaba wa PRNigeria Kan Ci Gaba da Tallafawa Matasa Wajen Sadarwa Bayan Karewar Tallafi
X whatsapp