Babban Bankin Najeriya, CBN ya yi watsi da raɗe-raɗin da wasu ke yaɗawa a ƙasar cewa daga ranar 31 ga watan Disamba mai zuwa za a daina amfani da tsoffin takardun kuɗin ƙasar.
Cikin wata sanarwa da CBN ɗin ya fitar ranar Alhamis ya ce wannan iƙirari ba gaskiya ba ne kuma ba shi da tushe balle makama.
”Bisa hukuncin ci gaba da amfanin da tsoffin takardun kuɗin da kotun ƙolin Najeriya ta yi a ranar 29 ga watan Nuwamban 2023, ta ce a ci gaba da amfani da takardun ba tare da iyakancewa ba”, in ji sanarwar.
Haka kuma sanarwar ta yi kira ga bankunan ƙasar su ci gaba da mu’amala da tsoffin takardun kuɗin.
Matakin na zuwa ne dai kwana guda da majalisar wakilan ƙasar ta yi kira ga CBN ɗin ya fara shirye-shiryen janye tsoffin takardun kuɗin daga zagayawa.
A shekarar 2022 ne dai tsohuwan gwamnatin Muhammadu Buhari, ta ɓullo da sabbin takardun kuɗin ƙasar na naira 200, da 500 da 1,000, sannan ta bayar da wa’adin daina amfani da tsoffin zuwa ƙarshen shekarar.
Batun ya haifar da ruɗani da tayar da hankali, inda daga baya wasu jihohin ƙasar suka shigar da ƙara a gaban kotun ƙolin ƙasar, wadda kuma ta jinkirta wa’adin, zuwa wani lokaci, inda daga baya ma ta ce a ci gaba da amfani da su ba tare da iyakancewa ba
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 18 hours 12 minutes 11 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 19 hours 53 minutes 36 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com