Shugaba Bola Tinubu ya nuna damuwarsa kan rashin wutar lantarki da arewacin Najeriya ke ci gaba da fuskanta.
Wata sanarwa da mai bai wa shugaban shawara kan harkar yaɗa labarai, Bayo Onanuga ya fitar, ya ce abin damuwa ne matuka ganin yadda ƴan yankin ke ci gaba da kasancewa cikin duhu kuma hakan na ƙara kassara ɓangaren tattalin arziki.
Tinubu ya ce yanzu yana jagorantar ƙoƙari da ake yi wajen ganin an gyara matsalar ta rashin lantarki.
Ya buƙaci ministan lantarki da sauran hukumomin da abin ya shafa da su gaggauta kammala aikin gyara turakun wuta da aka lalata da nufin mayar da wuta ga jihohin arewa.
“Ina cikin damuwa ainun kan rahotannin lalata wayoyin lantarki da sauran abubuwa da suka janyo rahin wuta,” in ji Tinubu.
Tinubu ya yi kira ga kamfanin rarraba wutar lantarki na Najeriya da su ƙoƙarta wajen ganin lantarki ta koma domin rage wa al’uma raɗadin da suke ciki.
Ya ce gwamnati ba za ta lamunci ci gaba da yin zagon ƙasa da kuma lalata turakun wutar lantarki ba.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 12 hours 20 minutes 59 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 14 hours 2 minutes 24 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com