Home Labarai NASSI ta bude hanyar neman Rancen Naira biliyan 75

NASSI ta bude hanyar neman Rancen Naira biliyan 75

Ƙungiyar masu ƙanana da matsakaitan Masana’antu ta Najeriya, wato Nigerian Association of Small Scale Industrialists (NASSI), ta bude hanyar neman rancen Naira Bilyan 75 da Gwamnatin Najeriya ta sahale musu.

Shugaban Kungiyar na kasa Chief Dakta Solomon Daniel Vonfa ne ya sanar da hakan, a yayin wani taron manema Labarai da ya jagoranta a Shelkwatar Kungiyar dake Babban Birnin tarayya Abuja, inda ya ce a yau suka bude shafin domin Mambobin kungiyar dama dukkan al’ummar Najeriya su nema.

Hanyar neman rancen ita ce “https://fgnboimsmeinterventionloan.boi.ng/ ” a inda wadanda zasu nema ta hannun Kungiyar kuma zasu fara yin rijista da kungiyar ta shafin “https://portal.nassi-ng.org/”.

Da yake karin haske, Babban Ma’ajin kungiyar na kasa, Dakta Abubakar Tanko Bala ya ce ga dukkan masu bukatar wannan rance zasu iya nema ta waccan hanya ko kuma su ziyarci Ofishin Kungiyar NASSI mafi kusa da shi.

Kungiyar ta kuma shawarci Mambobin ta dama dukkan al’ummar kasar da suyi amfani da wannan dama, domin bunkasa kasuwancin su dama samar karin kudin shiga ga kasar dama habbaka tattalin arzikin ta.

Taron manema Labaran ya sami halartar masu ruwa da tsakin Kungiyar na sassan Kasar dama tawagar Manyan Jami’an Bankin Masana’antu na Najeriya wato Bank of Industry, karkashin Jagorancin Hajiya Amina Habu.

A ranar 16 ga watan Oktobar nan ne Gwamnatin Najeriya ta amince da bawa mambobin kungiyar rancen Naira Bilyan 75, ta hannun Bankin Masana’antu domin su bunkasa kasuwancin su dama farfado da tattalin arzikin kasar.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa'adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDPAIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da ZamfaraSojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta'addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a SokotoCOAS Shaibu ya yi Kira da a Haɗa Kai Yayin da Sojoji Ke Faɗaɗa Zuwa Rukunoni 12Najeriya ta Shirya Horarwa ta Yankuna Kan Gano da Bin Diddigin Ƙananan MakamaiSojoji Sun Kai Harin Sama da ya Hallaka Ƴan ISWAP Sama da 40, ya Lalata Motoci a BornoAmurka ta Zargi Najeriya da Daukar Yara Sojoji, Masana'antun Jarirai da Fataucin MutaneHaɗaka DMI da TMS a London ta Tsara Sabuwar Hanyar Goyon Bayan Tinubu Zuwa 2027Yushau Shuaib @57: Bikin Jagora Wanda ya Buɗe Kofofi da Canza Rayuka Daga Hafsat Ibrahim Yusha'u Shuaib @57: Barka da zagayowar Ranar Haihuwa ga Jagoran Mazaje, Mutumin da Ya Bani Dama Daga Ozumi AbdulHarin Jirgin Sama a Filin Jirgin Saudiyya ya yi Sanadiyyar Mutuwar Mutane 12, Raunata 309Trump ya yi Kira ga Sabon Shugaban Ukraine, ya Zargi Zelensky da Kin Amincewa da Yarjejeniyar Zaman LafiyaAFRI-CIRD ta yi Kira ga Gwamnatoci su Kara Kudin Ilimin Ƴa'ya MataAmnesty International ta yi Allah Wadai da Toshe Taron 'Dole Tinubu Ya Tafi' da Ƴan Sanda Suka yi a KanoTMG vs TMS: Matsalar Sadarwa Kan Makomar Tinubu Daga Yushau A. Shuiba 
X whatsapp