Gwamantin tarayya Najeriya ta ce tana iya bakin kokarinta wajen dawo da wutar lantarkin yankin arewacin kasar da ta kwashe tsahon mako guda yana cikin duhu.
Ministan Makamashi, Adebayo Adelabu ne ya bayyana hakan, in da yace wutar yakin zata dawo aiki nan da kwanaki 14 masu zuwa.
yakin na arewaci na dauke da jihohi 17 wanda suka kasance cikin duhun rashin wutar tun ranar talata 12 ga watan Nuwamba, 2024.
Read Also:
Adelabu, yayi da yake amsa tambaya daga bakin wani sanata a majalisar tarayyar kasar, yace wani yanki na aikin zai kammala nan da kwanaki 3 masu zuwa.
A dai tsakanin nan ne Kungiyar tuntubar juna ta dattawan arewacin Najeriya, ACF ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta ayyana dokar ta-ɓaci kan ɓangaren wutar lantarki a daidai lokacin da yankin arewacin ƙasar ke ci gaba da kasancewa cikin duhu sakamakon rashin wuta.
Ƙungiyar gwamnomin arewacin Najeriyar ita ma ta yi kira ga gwamnatin Tarayya da ta gaggauta kawo ƙarshen matsalar.
PRNigeria Hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 12 hours 18 minutes 40 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 14 hours 5 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com