A karo na biyu kamfanin man Fetur na Nijeriya ya sake kara kudin Man abin da ya haifar da kace nace da mamaki bayan karin da yazo a ba zata ranar Talata 29 ga Oktoba 2024, wanda wannan shine Karo na biyu da kamfanin yayi ƙari cikin makonni uku.
Kamfanin man na kasa ya kara farashin daga naira 1,030 zuwa 1060 a Babban Birnin Tarayya Abuja, yayin da a Jihar Legas farashin ya koma Naira 1,025 daga 998 a kowacce lita.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Kafin wannan ƙarin, ana sayar da litar man fetur ne a kan N897 a Abuja, a Legas kuma N885, amma a ranar 9 ga watan Oktoba da muke bankwana da shi aka ƙara na Legas zuwa N998, na Abuja kuma zuwa N1,030.
Ķarin kudin na zuwa ne duk da fara aikin Matatar Man Ɗangote, wadda ake tunanin za ta kawo sauki da wadatuwar man a ƙasar.
Tun bayan da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sanar da janye Tallafin mai a watan mayun 2023, NNPCL ya ƙara kudin fetir daga 184 zuwa 1,025 a Jihar Legas.
Masana dai na ganin wannan wani mataki ne da zai kara jefa yan Najeriya cikin mawuyacin hali, dama tuni wasu suka ajiye ababen hawan su saboda tsadar farashin man.











